ABNA24 : Tuni wakilai daga kasashen duniya da dama suka iso birnin na Tehran domin halartar bikin.
A ranar Talata ne Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya mika wa zababben shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi takardar amincewarsa da zaben da aka masa a matsayin shugaban kasa.
An bayyana cewa wakilai daga kasashen duniya 73 zasu halarci bikin, wanda zai gaji shugaba Hassan Rohani mai barin gado.
bayanan da aka fitar, sun ce jami'ai 115 sun sanar da shirinsu na halartar bikin; daga cikin wadannan jami'ai, shugabannin kasashe 10, kakakin majalisar dokoki 20, ministocin harkokin waje 11, da wasu ministoci 10 daga kasashe daban-daban, da wakilai na musamman da mataimakan shugabannin majalisun dokoki, za su halarci bikin.
Sayyid Ebrahim Ra’isi ya lashe zaben shugabancin kasar ta Iran, da aka gudanar a ranar 18 ga watan Yuni da ya gabata.
342/